(ABNA24.com) Kamfanin dillancin labaran Saumaria News na kasar Iraki ya bayar da rahoton cewa, ofishin Ayatollah Sistani ya fitar da bayani da ke bayyana mahangarsa kan abubuwan da suke faruwa a kasar.
Bayanin ya ce, Ayatollah Sistani ya jaddada a kan batutuwa biyu, na daya daga cikinsu shi ne jama’a masu neman gyara da su yi amfani da hanyoyi na lumana, ba na tashin hankali ba.
Haka nan kuma ya kirayi jami’an tsaro da su kare masu zanga-zangar lumana domin neman a yi gyara a cikin harkokin tafiyarda mulkin kasar.
Baya ga haka kuma ya kirayi gwamnatin kasar da ta gaggauta aiwatar da sauye-sauye domin al’ummar kasar ta gani a kasa, kamar yadda ya yi kira da a gudanar da zabe da gaggawa.
/129
9 Faburairu 2020 - 10:35
Lambar labari: 1008910
Kamfanin dillancin labaran Saumaria News na kasar Iraki ya bayar da rahoton cewa, ofishin Ayatollah Sistani ya fitar da bayani da ke bayyana mahangarsa kan abubuwan da suke faruwa a kasar.